An tafka zazzafar muhawara karon farko tsakanin Trump da Harris

An tafka zazzafar muhawara karon farko tsakanin Trump da Harris

Trump ya yi kakkausar suka ga salon da Democrat ta yi amfani da shi wajen tunƙarar rikicin gabas ta tsakiya ya na mai cewa idan har da shi ne akan mulki ko shakka babu yaƙin da faruwa a Gaza ba zai taɓa faruwa ba.

A ɓangare guda Harris ta bayyana shirinta na samar da ƙasashe biyu da nufin warware rikicin tsawon shekaru tsakanin Isra'ila da Falasɗinu.

Dona Donald Trump da Kamala Harris yayin muhawara. AFP - SAUL LOEB

Dukkaninsu sun caccaki juna game da yadda Amurka ta tunƙari yaƙi da Taliban, inda Harris ta ce Trump ya tafka abin kunya bayan zaman tattaunawa da wakilcin mayaƙan na Taliban daga Afghanistan yayinda shi kuma soki gwamnatin Democrat kan yadda ta gaza cika alƙawarin kwashe Amurkawan da ke Ƙabul bayan Taliban ta ƙwace mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)