An tabbatar da wanda ya kai hari da wuka a Jamus na da alaka da DAESH

An tabbatar da wanda ya kai hari da wuka a Jamus na da alaka da DAESH

A harin wuka da mutane 3 suka rasa rayukansu a Würzburg, Jamus, an tantance asalin maharin.

An bayyana cewa, dan Somaliya Jibril A. mai shekaru 24, wanda ke zaune a garin tun shekarar 2015, yana karbar kulawar kwakwalwa na wani lokaci.

A cewar jaridar Bild ta Jamus, ‘yan sanda sun gano kayayyakin kungiyar ta’addanci ta DAESH yayin binciken gidan maharin.

A cewar kafafan yada labaran na Jamus, an kuma yi watsi da neman mafakar da maharin ya yi, amma ba a kore shi ba.

Wani mahari da wuka ya far wa masu wucewa da wuka a dandalin Barbarossa na Würzburg, mutane 3 sun mutu sannan mutane 6 sun ji rauni a harin.

'Yan sanda sun bayyana cewa maharin, wanda aka kama shi ta hanyar harbinsa da bindiga, bai cikin mawuyacin hali.

 


News Source:   ()