An tabbatar da Isra'ila ta aikata laifukan yaki a Gaza

An tabbatar da Isra'ila ta aikata laifukan yaki a Gaza

An sanar da cewa a hare-haren da Isra’ila ta kai wa Gaza, daga ranar 10 ga watan Mayu har na tsawon kwanaki 11 ta aikata laifin yaki.

A watan Mayu Isra’ila ta kai wani samame ne a Gaza, wanda ta kwashe tsawon shekaru 15 tana mamaya, inda Falasdinawa 260 da suka hada da yara 66 da fararen hula 129, suka rasa rayukansu.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch ta wallafa cikakken rahoton bincike kan abubuwan da suka faru.

A cikin wannan rahoton, kungiyar ta tabbatar da cewa Isra’ila ta aikata laifukan yaki.

Rahoton ya nuna cewa hare-haren da aka kai wa Gaza wani bangare ne na mamayar da Isra’ila ke ci gaba da yi.

Omar Shakir, Daraktan Kungiyar Isra’ila da Falasdinu na Kungiyar, ya ce, "Yana da mahimmanci a fahimci cewa wannan ta'addancin yana da yanayi mai fadi. Abubuwan da suka faru sun faru ne a daidai lokacin da aka rufe Zirin Gaza sosai ga duniya har na tsawon shekaru 14 domin nuna wariya don korar Falasdinawa daga gidajensu a Gabashin Kudus da aka mamaye." 


News Source:   ()