Ƴan Syria na shagulgular murnar hamaɓarar da gwamnatin Assad

Ƴan Syria na shagulgular murnar hamaɓarar da gwamnatin Assad

Shugaba Abu Mohammed al Julani da kansa ya buƙaci fitowar al’ummar ƙasar don gudanar da shagulgulan da ya bayyana dana ƴanci a birnin Damascus, bayanda ya jagoranci Sallar Juma’a yau ɗinnan a wani yanayi da ake dakon Firaminista Mohammed al-Bashir ya sanar da muƙarraban sabuwar gwamnatin da zai kafa duk dai a yau ɗin.

An ga yadda ƴan ƙasar ta Syria suka bazu akan tituna suka shagulgula yayinda wasunsu ke gudanar da addu’o’in samun nasara bayan da suka bayyana mulkin da ƴan tawayen za suyi a yanzu da cikakken ƴanci ga jama’a wanda ya kawo ƙarshen abin da suka kira da kama karyar mulkin iyalan gidan Assad na fiye da shekaru 50.

Wannan shagulgula na zuwa a daidai lokacin da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antonu Blinken ke ziyara a Turkiya guda cikin ƙasashen da ke goyon bayan tsagi ɗaya na ƴan tawayen Syriar inda ya nanatawa shugaba Recep Tayyib Erdogan buƙatar Amurka na kawar da mayaƙan IS a cikin ƙasar, ko da ya ke ya ce Washington a shirye ta ke ta mara baya ga Damascus amma bisa sharadin tabbatar da adalci ga kowanne ɓangare.

A gefe guda dubban ƴan Syria da ke hijira a ƙetare ne yanzu haka suka fara azamar komawa gida ko da ya ke wasu na ganin akwai buƙatar lokaci, don ganin salon kamun ludayin gwamnatin ƴan tawayen waɗanda suka alƙawarta gudanar da zaɓe a watan Maris na sabuwar shekara.

Ƙungiyar ƙwadago ta Jamus, ta bayyana cewa babu buƙatar tilastawa ƴan gudun hijirara Syria da ke zaune a Berlin komawa gida, domin galibinsu sun gina rayuwa a cikin ƙasar wanda zai musu matuƙar wahala su koma Damascus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)