Ƴan Syria miliyan guda ka iya komawa gida a farkon shekarar 2025- MDD

Ƴan Syria miliyan guda ka iya komawa gida a farkon shekarar 2025- MDD

A wani taron manema labarai da ta kira a birnin Geneva, daraktar hukuma kula da ‘yan gudun hijra ta Majalisa Dinkin Duniya mai kula da shiyyar Gabas ta tsakiya da arewacin Afirka Rema Jamous, ta ce hasashen su ya nuna cewa daga watan Janairu zuwa Yunin shekara mai kamawa akalla ‘yan gudun hijra Syria mutum miliyan guda ka iya komawa gida.

Wani jami’i a hukumar HCR ya roki kasashen duniya  su daina tilastawa ‘yan gudun hijrar komawa gida, tare da jiran zuwa lokacin da lamurra za su daidaita a ƙasar.

Kasar Turkiya ke karbar kashi 50% na adadin ‘yan Syria aƙalla mutum miliyan 6 da ke warwatse a sasan duniya bayan ta'azzarar yaƙin ƙasar da ya faro a shekarar 2011.

Sauran kasashen da suka baiwa ‘yan Syria mafaka sun hada da Jamus da Lebanon baya ga Jordan da Masar da kuma Australiya sai kuma Sweden.

Tuni Majalisa Dinkin Duniya da tawagogin jami’an diflomasiyar kasa da kasa suka isa Damascus baban birnin Syria da zummar ganawa da sabbin mahukuntan wannan kasar da yakin shekaru 13 ya tagayyara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)