An soke Bukin Venice na bana

An soke Bukin Venice na bana

An soke Bukin Venice wanda ake gudanarwa a watan Fabrairun kowace shekara a Italiya, a wannan shekarar kamar yadda aka yi a bara saboda sabon nau'in kwayar cutar corona (Covid-19).

Ba kamar yadda ya ke a da ba, a halin yanzu babu mutane a titunan Venice bayan da aka soke bukin wanda ke sa dubun dubatan masu yawon bude yin tururuwa zuwa birnin a watan Fabrairu.

An soke Bukin na Venice a shekarar da ta gabata saboda karuwar yawan mutanen da ke kamuwa da kwayar cutar corona, yayin da annobar Covid-19 ta fara tsanani a Italiya.


News Source:   ()