A gwanjon kayayyakin da aka yi a birnin New York dake kasar Amurka an siyar da kwarangwal din dabbar dinosaur mai shekaru miliyn 67 akan zunzurutun kudi har dala miliyan 27.5.
A gidan ajiye kayan tarihin Christie dake New York anka fitar da wani kwarangwal din dabbar dinosaur mai suna T-rex (Tryannosaurus) domin siyarwa.
A tayin da aka yi na mintuna 10 aka samu wanda ya sayi gwarangwal din dabbar dinosaur mai shekaru miliyan 67 da kudi dala miliyan 27.5.
Tare da haraci da sauran kudaden da ya biya kudin kwarangwal din dabbar dinosaur din ya kai dala miliyan 32.
Sikeletan dinosaur din mai tsayin mita 11.27, wanda aka kiyasta zai kai kimanin dala miliyan 8 kafin a siayar dashi, mallakar Black Hills Geological Research Institute ne dake Dakota ta Kudu.