An sanar da cewa mai fafatukan kare hakkokin bil adama kuma mai adawa da gwamnatin Rasha Aleksey Navalnıy da aka kwantar asibiti akan tunanin an sanya masa guba an kai shi Jamus.
Mai magana da yawun Aleksey Navalnıy wato Kira Yarmış ya yada a shafukan sadar da zumunta da cewa matar Navalniy wato Yulya Navalniy ta bayyana cewar an kai mijinta a birnin Berlin dake Jamus.
Za'a ci gaba da jinyar Navalnıy a wata asibitin koyarwa ta wata jami'a mai zaman kanata.
A yayinda yake tafiya daga birnin Tomsk zuwa Moscow a ranar 20 ga watan Agusta Navalniy ya kasance cikin rashin lafiya mai tsanani lamarin da ya snyashi sauka a birnin Omsk.
Ana dai zargin cewa an sanya masa guba ne a cikin wani shayin da ya sha.