Ta cikin wata sanarwa da mataimakin babban daraktan binciken manyan laifuka na ƙasar Don Freeman ya sanyawa hannu ta ce ana zargin magidancin da hallaka ɗansa.
Mr Olawusi wanda yanzu haka ya ya cika wandonsa da iska bayan tserewa daga hannun jami’an tsaro, na fuskantar tuhumar aikata manyan laifuka da suka haɗar da kisan gilla matakin farko.
Bayanai sun ce ƴan sanda sun sami gawar yaron cikin jini bayan faruwar lamarin a watan Afrilun 2017 a yankin Rhodes Island, inda yake zaune.
Jami’an tsaro sun ce da alama ya lakaɗawa yaron dukan kawo wuƙa ne, kuma lokacin da suka isa wajen sun tarar da yaron da sauran numfashi, amma kafin a kai shi asibiti a cika.
Aƙalla asibitoci 18 da gwamnati ta baiwa damar gudanar da bincike kan gawar yaron sun ce ya mutu ne a sakamakon duka, kuma ya sami raunuka sama da 18 a sassan jikinsa.
Kwanaki kaɗan bayan mutuwar yaron ne jami’an tsaro suka chafke mahaifin nasa amma kuma aka sake shi a wannan rana da nufin faɗaɗa bincike, ba kuma tare da ɓata lokaci ba ya tsere.
Ana dai zargin Mr Olawusi da haɗin bakin abokansa da iyalansa ya bar ƙasar, inda yabi ta filin sauka da tashin jiragen sama da John .F. Kennedy da ke birnin New York a ranar 20 ga watan Yulin 2017.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI