Alkalamun bunkasar masana'antum kasar Turkiyya ya nuna karuwar kaso 1.3 cikin dari a watan Disamba da kuma kaso 9 cikin dari a shekarar 2020.
Hukumar Kididdigar Kasar Turkiyya ce ta sanar da cewa an samu bunkasar masana'antun kasar Turkiyya a 2020 idan aka kwatanta da na shekarar 2019.
Fannin kere-kere ya bunkasa da karuwar kaso 12.1 cikin dari.
Kanfunan dake karkashin masana'antun kere kere kamar su na hakar ma'adanai sun karu a watan Disamba 2020 da karuwar kaso 6 cikin dari. Haka kuma fannin samar da wutar lantarki da iskar gas ya bunkasa da kaso 4.9 cikin dari a shekarar bara.