An samu raguwar rashin aikin yi a Amurka

An samu raguwar rashin aikin yi a Amurka

Kasancewar bunkasa harkokin kiwon lafiya da kuma bude ma’aikatu da akayi an bayyana cewa yawan wadanda ke cika fom din neman tallafin rashin aikin yi ya ragu sosai a cikin watanni hudun da suka gabata.

Duk da dai matsalolin da Korona ta haifar zai dauki lokaci gabanin a magancesu ana samun raguwar rashin aikin yi a kasar ta Amurka.

A watan Febrairu dai mutum miliyan 20.1 ne suka yi rajistan karbar kudin tallafi sakamakon rashin aikin yi a fadin kasar.

Masanin tattalin arziki a kasar Amurka Robert Frick ya bayyana cewa muna daf ga rage rashin aikin yi amma da sauran rina a kaba. Ya bayyana hakan ne a taron harkokin kudi da aka gudanar a Vienna. Yayinda ya kara da cewa muna fatan samun raguwar mace-mace daga Korona lamarin kuma da zai sanya karin samun aiki a kasar.


News Source:   ()