Hukumar yaki da yaduwar cututtuka a Amurka ta ba da rahoton mafi karancin adadin wadanda suka kamu da cutar coronavirus da mace-mace tun lokacin da cutar ta bulla.
Cibiyoyin Kula da Cututtuka sun ce yawan sabbin masu kamuwa da cutar ya ragu zuwa kusan 15,600 a kowace rana - matakin da ya yi kasa tun watan Maris din shekarar 2020.
Duk da haka, shugabar CDC, Rochelle Walensky, ta fada a Fadar White House cewa "labarai ne da nake son isarwa kuma tabbas wadannan bayanai suna karfafa gwiwa da kuma daukaka."
Ta ce an samu raguwar masu kamauwa da Korona da kaso 30 cikin darin a cikin kwanaki bakwai da suka gabata kuma da raguwar kaso 94 cikin dari tun daga watan Janairu.