Kasar Pakistan ta bayyana cewa ta samu mafi karancin wadanda suka kamu da corona a kasarta a cikin watanni uku da suka gabata.
An bayyana cewar a cikin awanni 24 da suka gabata mutum 900 aka samu dauke da kwayar cutar.
Da mutum 903 da aka samu cikin awanni 24 yawan wadanda suka kamu da cutar sun kai dubu 278, 305 inda kuma 1,146 suke cikin mawuyacin hali kamar yadda ma’aikatar lafiyar kasar ta bayyana.
Wannan ne mafi karancin yawan wadanda aka samu da cutar a rana tun a ranar 14 ga watan Mayu da kasar ta bayyana samu mutum 490 dauke da cutar.