Rahoton da ma’aikatar cikin gidan Birtaniya ta wallafa a wannan Laraba, ya nuna cewar ‘yan ci rani dubu 36 da 816 suka tsallaka mashigin ruwan dake tsakanin ƙasar da Faransa a shekarar bara, adadin da ya zarta na ‘yan ci ranin dubu 29 da 437, da suka kwarara cikin Birtaniyar a shekarar 2023.
Sai dai duk da ƙarin kwankwacin kashi 25 na kwararar ‘yan ci ranin ta hanyar amfanin da ƙananan jiragen ruwa da Birtaniyar ta gani, adadin bai kai mafi ƙololuwea da ƙasar ta yi fama da shi ba na baƙin-hauren dubu 45 da 774 a shekarar 2022.
Akalla mutane 76 suka mutu yayin haɗurran jiragen ruwan ‘yan ci ranin kusan 20 da aka samu a bara, yayin da Faransa ta ce mutane kusan dubu 6000 jami’anta suka ceto daga halaka cikin teku a dai shekarar ta bara.
Shige da ficen baƙi da kuma na kwararar ‘yan ci rani ba bisa ƙa’ida ba dai na daga cikin manyan batutuwan da suka yi tasiri a babban zaɓen Birtaniya na watan Yuli da ya maido da jam’iyyar Labour kan mulki a ƙarƙashin jagorancin Firaminista Keir Starmer, bayan shafe shekaru 14 tana adawa.
A halin yanzu an zura idanu don ganin irin matakan da gwamnatin jam’iyyar Labour za ta ɗauka don kawo ƙarshen matsalar kwararar ta ‘yan ci rani.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI