Masu bincike a Jami'ar Oxford ta Ingila sun fitar da sakamakon gwaji na 2 na allurar riga-kafin zazzabin cizon sauro mai suna "R21/Matrix-M" da suka samar.
Sakamakon gwajin ya bayyana cewa, a tsawon watanni 12 an ga yadda allurar riga-kafin ta ke da tasiri da kaso 77 cikin 100, ana sa ran nan da shekaru 2 za a bayar da izinin sayar da ita ga kasashen duniya.
Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa, kaso 75 cikin 100 na tasirin allurar riga-kafin zazzabin cizon sauro ake bukata a duniya.
Daraktan Cibiyar Bincike ta Jenner wadda AstraZeneca-Oxford ke kula da ita Farfesa Adrian Hill ya shaida cewa,
"A shekarar da ta gabata zazzabin cizon sauro ya yi ajalin mutane a Afirka ninki 4 sama da cutar Corona."
Hill ya ja hankali da cewa, ana bukatar bayar da izinin gaggawa don fara amfani da allurar riga-kafin a Afirka, gwaji na 3 zai dauki tsawon shekaru 3 zuwa 5, kuma a wannan lokaci za a yi wa yara kanana a Afirka dubu 300 allurar.
Cutar zazzabin cizon sauro na kashe yaro 1 a duk mintuna 2 a duniya, kuma an fi samun bullar ta a kasashen Afirka.
A kasashen Gana, Kenya da Malawi an yi gwajin allurar riga-kafin zazzabin cizon sauro da aka kirkira a karon farko mai suna "RTS,S". An bayyana yiwa sama da mutane dubu 650 allurar.