An samar da gilashi da ya fi lu'u-lu'u karfi a kasar China

An samar da gilashi da ya fi lu'u-lu'u karfi a kasar China

A China an samar da wani gilashi mafi karfi kuma mafi juriya a duniya.

Masana kimiyyar kasar China sun murkushe tare da hada sinadarin fullerene don samar da gilashin. An yi amfani da matsanancin zafi da karfin digiri Celsius 1200.

Wannan sabon gilashin wanda aka ce yana da ban mamaki yana da amfani a aiyukan inji da kayan lantarki kuma an sanya masa suna AM-III.

An kwatanta sabon gilashin da lu'u-lu'u.

Bincike ya nuna cewa taurin gilashin ya kai gigapascals 113, yayin da lu'u-lu'u ya ke ba da sakamakon 50 zuwa 70 a cikin gwaji ɗaya.

Gilashin wanda ya fi lu'u-lu'u tauri, ana iya amfani da shi a fannoni daban-daban ciki har da batira masu amfani da hasken rana.


News Source:   ()