An zabi Farfesa Dakta Sevil Atasoy a matsayin mamba ta Kwamtin Kula da Magunguna ta Majalisar Dinkin Duniya (UN) a karo na uku.
An sake zaben Sevil Atasoy a matsayin mamba ta kwamitin da ke Vienna don aiki daga shekarar 2022 zuwa 2027 a zabukan da aka gudanar a Zauren Majalisar Dinkin Duniya kan Tattalin Arziki da Zamantakewa.
Atasoy wacce ta fara aiki a Kwamitin Kula da Magunguna ta Majalisar Dinkin Duniya daga shekarar 2005 zuwa 2010, ita ce 'yar kasar Turkiyya na farko da ta zama shugabar hukumar.
Kwamitin yana da mambobi 13.