An sake zabar Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin shugabar WTO

An sake zabar Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin shugabar WTO

WTO wadda ke da shalkwata a Geneva na kasar Switzerland, ta tabbatar da jagorancin Okonjo-Iweala a karo na biyu, a shafinta na X

A watan Satumba ne, Okonjo-Iweala, mai shekaru 70, ta ayyana kudirinta na sake tsayawa takarar shugabancin kungiyar a karo na biyu.

Dama shugaban majalisar gudanarwar kungiyar, Ambasada Petter Ølberg dan kasar Norway ya shaidawa mambobin kungiyar cewa za ta sake tsayawa takara, amma har zuwa lokacin karewar wa'adin masu neman mukamin, babu wanda ya mika bukatar fafatawa da ita.

A cewar kungiyar, jagorancin nata karo na biyu zai fara aiki ne ranar 1 ga Satumba, 2025.

Nadin babbar daraktar ya zo ne bisa yarjejeniya tsakanin kasashe 166 mambobin kungiyar ta WTO.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)