An yi nasarar gwayin jirgin Roc mai fika-fikai mafi tsayi a duniya karo na biyu a kasar Amurka.
Fikafikan jirgin dake shawagi a hamadar Mojave a jihar Kalifoniya sun kai mita 117, wadanda suka fi girman na jirgin Boeing 747 har sau biyu.
Tagwayen jirgin mai inji 6 zai yi tashi har ya kai nisan kafa dubu 35, yana iya daukar kayayyaki masu nauyin ton 250 wanda kuma zai iya sauri fiye da karar sauti har sau biyar.
Jirgin na Roc da aka yi don jigilar jiragen Hypersonic, haka kuma za a yi amfani da shi a binciken sararin samaniya.
An yi gwajin jirgin Roc din na farko ne a watan Afrilun shekarar da ta gabata.