A garin Kalyubiye kasar Masar kaucewar wani jirgin kasa daga layin dogo yayin sanadiyar rayukan fasinjoji 8 da kuma raunanan fiye da 100.
Kamar yadda Hukumar Kula da Jiragen Kasa a kasar Masar ta sanar jirgin kasa mai lamba 949 a yayinda yake kan hanyarsa daga Alkahira zuwa Mansura ya kauce daga layin dogo a daidai garin Kalyubiye lamarin da ya sanya ficewa wagon hudu.
Sanarwar ta kara da cewa a halin yanzu an samu rasuwar mutum 8 inda kuma fiye da 100 suka raunana.
Tuni dai ma'aikatar bayar da agajin gaggawa sun bayyana a yankin domin bayar da ceto.
A ranar 26 ga watam Maris ma an samu hatsarin jirgin kasa a kasar Masar lamarin da ya yi sanadiyar rayukan mutum 32 da raunanan wasu 66.