An sake tsare tsohon lawyan shugaban kasar Amurka Donald Trump watau Michael Cohen wanda aka mayar gida daga gidan wakafi sanadiyar kwayar cutar Covid-19.
Lawyan Cohen ya bayyana cewa an tsare shi ne sanadiyar sabawa ka'idojojin gidan yari da aka sharada masa gabanin mayar dashi a gida.
An saki Cohen da zummar ya karasa sauran kwanakin da aka yanke masa wanda zai yi a gidan yari a gidansa sabili da barkewar sabuwar kwayar cutar da aka samu a gidan wakafin da yake tsare.
An yankewa Cohen hukuncin daurin shekaru uku ne a watan Mayun shekarar 2019 a gidan yarin Otisville sanadiyar kama shi da aka yi da laifin yin karya a yayin gudanar da bincike akan zaben shugaba Trump da kuma laifin kin biyan haraji.
Cohen mai shekaru 53 zai kammala zaman gidan yarinsa ne a watan Nuwamban shekarar 2021.