An sake buɗe Hasumiyar Eiffel da ke Faransa wacce aka rufe saboda sabon nau'in kwayar cutar corona (Covid-19), bayan watanni 9.
An rufe Hasumiyar Eiffel, daya daga cikin shahararrun alamomin kasar ga maziyarta a wani bangare na matakan da aka dauka saboda barkewar Covid-19.
Masu yawon bude ido, wadanda ke son hawa zuwa hasumiyar wacce aka sake budewa yau bayan watanni 9, sun yi dogayen layuka a gaban rumfunan karbar kudaden shiga.
An takaita adadin mutanen da ake bari su shiga cikin hasumiyar zuwa mutane 1,300 a kowace rana, a wani banagare na aiki da dokar nisanta da juna.
Bugu da kari, an bayyana cewa za a nemi maziyarta su nuna sakamakon gwajin PCR kafin a bari su shiga cikin hasumiyar daga mako mai zuwa.