Akalla mutane 30 aka kashe a hare -haren bindiga da aka kai a jihar Filaton Najeriya da ke Yammacin Afirka.
An kai hare -hare da makamai a daren jiya a kauyuka 3 na lardin Plateu.
Akalla mutane 30 ne suka mutu a hare -haren, da dama sun jikkata, sannan an kona gidaje da dama.
Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na jihar Filato Makut Macham ya ce a cikin rubutacciyar sanarwa cewa an tsare mutane 10 dangane da harin.
Macham ya bayyana cewa Gwamnan Filato Simon Lalong ya ayyana dokar ta-baci a yankunan tare da kiran taron gaggawa.