A jihar Osun dake kasar Najeriya an yi awon gaba da Chinawa biyu tare da neman kudin fansa.
Kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka rawaito wasu wadanda ba'a san ko su wanene ba sun kai hari a kauyen Okepa/Itikan inda ake hakar ma'adanai a jihar Osun.
A harin an yi awon gaba da yan kasar China mutum biyu, haka kuma jami'an tsaro biyu dake yankin hakar zinaren sun raunana sakamakon harin.
Tuni dai an fara kai farmakin kubutar da wadanda aka sacen tare da kuma kamo maharan.
A watanni biyu da suka gabata ma an kai hari a jihar Osun tare da sace Chinawa uku da kuma kashe jami'in tsaro daya.
A jahohin kasar Najeriya da dama, duk da dai an kaddamar da dokar hukuncin kisa ga masu satar mutane domin karbar kudin fansa, haka ba ta cimma ruwa ba.