An sace alluran rigakafin Korona a lran

An sace alluran rigakafin Korona a lran

An kai hari kan wata mota dauke da  maganin allurar rigakafin Korona (Kovid-19) a Tehran, babban birnin Iran. An sanar da cewa mutanen da suka kai wa motar hari sun sace allurai 300.

An kai hari kan wata mota dauke da alluran rigakafin cutar coronavirus bayan da ta bar ma'adanan Ma'aikatar Lafiya ta Iran a yankin Yaftabad.

Maharan sun sace allurai 300 na allurar Kovid-19, bayan sun yiwa direban motar doka.

Shugaban 'yan sandan Tehran Hussein Rahimi da Babban Manajan Hulda da Jama'a na Ma'aikatar Lafiya Kiyanus Cihanpur ne suka tabbatar da labarin cewa an sace alluran rigakafin.

Shugaban ‘yan sanda Rahimi ya ce ana ci gaba da kokarin cafke barayin.


News Source:   ()