An rusa muhimmiyar gadar yankin Tigray a Habasha

An rusa muhimmiyar gadar yankin Tigray a Habasha

Kwamitin Ceto na Kasa da Kasa ya ba da rahoton cewa gada daya tilo da ke kan Kogin Tekeze a arewacin Habasha da ya hada yankin Tigrai da Amhara, inda nan ne kungiyar ‘Yan tawayen‘  Kabilar  Tigray suke an rusa shi.

A cikin bayanin da kwamitin ya yi, an bayyana cewa rusa gadar zai kara kawo cikas ga taimakon da kungiyoyin agaji ke bayarwa ga yankin Tigray, wanda ke fuskantar yunwa, ga kusan mutane dubu 900.

Duk da cewa ba a san wanda ya rusa gadar ba, an yi ta rikici tsakanin gwamnatin Habasha da sojojin yankin na tsawon lokaci a yankin.

A gefe guda kuma, babu wani bayani a hukumance da aka yi game da gadar da aka lalata har izuwa yanzu.

Gwamnatin Habasha ta sanar a ranar 28 ga watan Yuni cewa ta ayyana tsagaita wuta a wani yanki a yankin Tigray, wanda ake zargin ‘yan tawayen TPLF sun kame.

Fiye da mutane miliyan 1 ne suka rasa muhallansu a lardin bayan da sojojin TPLF masu tawaye, wadanda a da ke mulkin lardin Tigray, suka kai hari kan sojojin Kwamandan Arewacin Habasha a ranar 3 ga watan Nuwamba, 2020, kuma bayan firaiminista Abiy Ahmed ya yanke shawarar daukar matakin soja a kan kungiyar ta TPLF.


News Source:   ()