An rufe dukkan makarantun a jihar Zamfara bayan da 'yan bindiga suka sace dalibai da dama a jihar.
Jami’in ‘yan sanda Ayuba Elkana ya sanar da cewa bayan sace dalibai daga jihar Zamfara ta Najeriya, Gwamna Bello Matawalle ya umarci dukkan makarantun yankin su kasance a rufe har sai an samu sanarwa.
Elkana ya kuma ce an ayyana dokar hana fita a gundumomi 13 na jihar tsakanin karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe agogon kasar.
An yi garkuwa da dalibai da dama a harin da 'yan bindiga suka kai da safiya a makarantar jeka-ka-dawo ta Kaya dake garin Maradun a jihar ta Zamfara.