An rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban Amurka a karo na biyu

An rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban Amurka a karo na biyu

Bikin rantsuwar da aka gudanar a ɗakin taro na majalisar dokokin Amurka ya samu halatttar manyan mutane daga ciki da wajen Amurka.

A jawabin da shugaba Trump ya yi jim kaɗan bayan rantsar da shi, ya zayyano manyan ƙudirorin da zai mayar da hankali a gwamnatinsa. inda ya sha alwashin dawo da martaba da daraja da ƙima ta Amurka a idon duniya.

Ya ce zai tabbatar da tsaro a cikin ƙasar a matsayinsa na shugaban ƙasa.

Bikin rantsar da abon Shugaban Amurka Donald Trump da mataimakinsa JD Vance Bikin rantsar da abon Shugaban Amurka Donald Trump da mataimakinsa JD Vance REUTERS - Kevin Lamarque

Shugaba Trump ya sha alwashin tabbatar da haɗinkan jama'ar Amurka tare da kawo sauye-sauye a ƙasar domin ta ci gaba da yin fice a duniya.

Ya bayyana alfaharinsa da cewa kwana guda kafin rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa an tsagaita wuta a yakin da ake gwabzawa a Gabas ta Tsakiya.

Sabon shugaban na Amurka Trump ya bayyana abu na farko da zai mayar da hankali a kai shine tabbatar da korar duk wasu baƙi da ke zaune a ƙasar ba bisa ka’ida ba.

Ya kuma nanata cewa tabbas Amurka za ta ƙara zama mai kuɗin gaske a karƙashin mulkinsa.

Muhimman matakan  da Trump ya bayyana cewa zai zartar a gwamnatinsa

- Ya sanya dokar ta ɓaci a iyakokin kudancin Amurka tare da tura dakaru don daƙile kwararar baƙi

- Zai kori dumbin bakin da ke Amurka

- Ya sanya dokar ta ɓaci dangane da haƙo mai domin rage farashin makamashi a Amurka

-Kawo ƙarshen ƙudirin kare muhalli da wajabta amfani da motoci masu lantarki

- Ƙirƙirar hukumar tattara haraji daga ƴan ƙasashen waje

- Zartar da ƙudirin cewa gwamnatin Amurka jinsi biyu kawai ta sani a hukumance, Namiji da Mace wato babu Mata Maza

-Kafa tutar Amurka a duniyar Mars

- Zai ƙwace iko da mashigin ruwa na Panama Canal

-Sauya sunan gabar ruwan Maxico zuwa gabar ruwan Amurka

-Sauya sunan tsaunin Denali zuwa McKinley

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)