Andy Ogles ya gabatar da ƙudirin ne a yayin zaman majalisar na jiya alhamis, inda ya ce akwai buƙatar a yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar kwaskwarima don bai wa Trump dama.
A cewarsa, shugaba Trump ya nuna cewa zai iya maido da martabar ƙasar, don haka ya ce yana kyau a bashi dama don cimma ƙudirinsa.
Ya na da kyau mu bai wa Trump isasshen lokacin da ya kamata don gyara kurakuren da gwamnatin Biden ta tabka, don haka a matsayinmu na ƴan majalisa ya kamata mu ba shi goyon bayan daya kamata.
Andy Ogles ya kuma yaba da matakin Trump na sanya hannu kan wasu dokar zartarwar shugaban ƙasa da ya yi a ranar da aka rantsar da shi.
A baya dai shugaba Trump ya ƙaryata duk wata jita-jita da ake yi cewa zai nemi wa’adi na uku, duk da cewa a lokacin wata ganawa da ya yi da ƴan majalisar dokokin ƙasar ƴan jam’iyar Republican bayan nasarar lashe zaɓen wa’adi na biyu da ya yi, ya ce ba zai sake tsayawa takarar ba, har sai in sunyi wani abu akai.
A shekarar 1947 ce dai aka gabatar da kudirin sashin na 22 na ƙundin tsarin mulkin ƙasar, kuma an amince da shi ne a shekarar 1951, don hana shugaba Franklin Roosevelt sake tsayawa takara.
Sau hudu Roosevelt na lashe zaɓen shugabancin ƙasar daga tsakanin shekarar 1933 zuwa 1945, sai dai ya mutu a shekara ta 1945, ƙasa da kwanaki 90 bayan rantsar da shi a wa’adi na hudun.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI