'Yan ta'adda uku daga kungiyar' yan ta'addar aware ta PKK, wadanda aka gano a yankin Metina da ke arewacin Iraki an magance su.
A cikin sanarwar da aka fitar a adireshin Twitter na Ma'aikatar Tsaro ta Kasar Turkiyya, an bayyana cewa, an gano 'yan ta'addar PKK 3, a Metina da ke arewacin Iraki sakamakon aikin hadin gwiwa na Sojojin Turkiyya da Hukumar Leken Asiri ta Kasa (MIT).
An bayyana nasarar magance 'yan ta'adda a wani farmaki da aka kai wa kungiyar ta sama.
A cikin sanarwar an kara da cewa,
"Za mu ci gaba da murkushe 'yan ta'adda a cikin dakunan su ba tare da gajiywa ba"