An magance wasu 'yan ta'adda biyu daga mambobin kungiyar ta'addar aware ta PKK a Faramakin Kambori-Walkiya da ake ci gaba da gudanarwa a yankin Avasin-Basyan da ke arewacin Iraki.
A cikin sanarwa mai taken "Muna ci gaba da shiga cikin ramin su" daga shafukan sada zumunta na Ma'aikatar Tsaron Kasar Turkiyya an bayyana cewa,
"Jaruman sojojinmu na Turkiyya sun kashe 'yan ta'addar PKK 2 a wani bangare na Farmakin Kambori-Walkiya da ake gudanarwa a yankin Avasin-Basyan da ke arewacin Iraki."
A gefe guda kuma, tare da aikin Kungiyar Leken Asiri ta Kasar Turkiyya (MIT) a garin Sulaymaniyah a Iraki,an yi nasarar magance wani dan ta'adda da ake nema ruwa a jallo mai suna Ulas Dogan.