Ma'aikatar harkokin tsaron kasar Turkiyya ta sanar da cewa an magance wasu mambobin kungiyar ta'addar PKK/YPG 3 a yankunan da aka gudanar da farmakan Garkuwar Firat da Tafkin zaman lafiya.
Kamar yadda ma'aikatar ta sanar an magance mambobin kungiyar ta'addar PKK/YPG 3 a yayinda suke yunkurin tayar da hankula a yankunan da aka gudanar da Farmakan Tafin Zaman Lafiya da Garkuwar Firat.
Kwamandojin Turkiyya ne dai suka yi nasarar magance 'yan ta'addan ta hanyar bude musu wuta gabanin su kai harin da suke shiryawa.