An magance 'yan ta'addan PKK/YPG 3 a Siriya

An sanar da nasarar magance mambobin kungiyar ta'addar PKK/YPG 3 a yankin da aka kaddamar da farmakin tafkin zaman lafiya a Siriya.

Ma'aikatar tsaron kasar Turkiyya ce ta sanar a shafinta ta twitter da cewa ba za'a ttaba bayar da izini ga kungiyar ta'addar PKK/YPG ta hana sukuni a yankin ba.

Sanar ta kara da cewa a farmakin da aka kai yankin an yi nasarar magance mambobin kungiyar ta'addar PKK/YPG uku. Za'a dai ci gaba da kai farmakai a yankin domin samar da zaman lafiya mai dorewa.

 


News Source:   ()