Sojojin Turkiyya sun kashe 'yan ta'adda 6 wadanda mambobi ne na kungiyar ta'addar aware ta PKK/YPG a arewacin Siriya.
A cewar sanarwar da ma'aikatar tsaron kasar Turkiyya (MSB) ta fitar, an kashe 'yan ta'adda 6 bayan arangamar da aka yi a yankunan Zavyan da Shaalah, Tel Cican da Tel Unayb da ke gabashin birnin Tel Rifat a Siriya.
An tabbatar da cewa daya daga cikin ‘yan ta’addan da aka kashe shi ne wanda ya kai hari kan motar daukar marasa lafiya a yankin a ranar 5 ga watan Agusta, inda mutane biyu suka rasa rayukansu.