An sanar da nasarar magance wasu 'yan ta'addan PKK 5 a yankin Gara dake Arewacin kasar Iraki.
Ma'aikatar harkokin tsaron kasar Turkiyya ce ta bayyana cewa,
"A wani farmakin da rundunar sojan Turkiyya da hadin gwiwar hukumar leken asirin kasar suka gudanar, an magance 'yan ta'addan PKK biyar a yankin Gara dake arewacin kasar Iraki. Za a kuma ci gaba da yaki da ta'addanci ba dare ba rana"