An kashe 'yan ta'adda uku daga cikin mambobin kungiyar ta'addar aware ta PKK da aka gano a yankin Hakurk a arewacin Iraki.
A wata sanarwa da aka fitar a shafin Twitter na Ma’aikatar Tsaron Kasar Turkiyya an yi luguden wuta akan gungun 'yan ta'adda. Inda aka kara da cewa,
"Sakamakon farmakin Sojojin Turkiyya da hadin gwiwar Hukumar Leken Asirin Kasar, an sake gudanar da wani aiki cikin nasara. An kashe 'yan ta'addar PKK 3 da aka gano a yankin Hakurk da ke arewacin Iraki ta hanyar kai musu hari ta sama."