A Najeriya an kaddamar da farmaki akan kungiyar ta'addar Boko Haram inda aka yi nasarar kashe mutum 9 daga cikinsu.
Mai magana da yawun ma'aikatar tsaron kasar Najeriya Bernard Onyeuko ya sanar da cewa kungiyar ta kai farmakai akan kungiyar ta'addar Boko Haram a jihar Borno.
Onyeuko ya kara da cewa baya ga mambobin Boko Haram 9 da aka kashe da yawansu sun tsere da raunuka a jikinsu.
Ya kuma kara da cewa an lalata mabuyar 'yan ta'adda da kuma guraren da suke adana makamai.