An sanar da cewa an kwantar da tsohon Firaministan Italiya, Silvio Berlusconi a asibiti tun ranar Litinin.
Ba a yi wani bayani dangane da rashin lafiyar Berlusconi mai shekaru 84 ba.
Da yake magana da kamfanin dillacin labaran Birtaniya na Reuters, daya daga cikin majiyoyin ya bayyana cewa halin da Berlusconi yake ciki ba mai tsanani ba ne.
An bayyana cewa tsohon Firaministan ba zai iya halartar wani taron jama'a ba na wani lokaci.
Berlusconi ya kamu da sabon nau'in kwayar cutar corona (Covid-19) har sau 2 a baya.