An sanar da cewa an kwantar da Sarkin Kuwait Sheick Sabah el-Ahmed el-Jabir es-Sabah domin duba lafiyarsa.
Kamar yadda kanfanin dillancin labaran kasar Kuwait ta (KUNA) ta sanar shugaban fadar kuma ministan cikin gidan kasar Sheick Ali Jerrah As Sabah ya sanar da cewa an kwantar da Sarki As Sabah a asibiti domin sake duba lafiyarsa.
Minista es-Sabah, bai bayyana irin halin rashin lafiyar da sarkin ke fama da shi ba.
Sarkin Katar dai ya kwanta a asibitin a kasar Amurka a watan Oktoban 2019 domin duba lafiyarsa.