An kwantar da Paparoma Francis, shugaban mabiya darikar Katolika ta duniya, a asibiti saboda wani aikin tiyata da aka shirya yi masa.
Mai magana da yawun Vatican, Matteo Bruni wanda ya gabatar da bayani game da batun ya bayyana cewa za a yi wa Paparoma Francis mai shekaru 84 aikin tiyata sakamakon cutar hanji.
Kakaki Bruni bai bayar da cikakken bayani game da lokacin da za a yi aikin a asibitin Gemelli da ke Roma, babban birnin Italiya ba.