An ceto bakin haure masu yunkurin zuwa Turai ba bisa ka'ida ba, galibi 'yan Afirka, a gabar tekun Morocco.
A cewar labarin kamfanin dillacin labarai na MAP, rukunin masu gadin gabar teku sun ceci bakin haure 368 wadanda ke neman zuwa Turai ba bisa ka'ida ba a ranar 20-23 ga watan Yulin.
An lura da cewa bakin haure da suka fito daga Afirka kuma suna ƙoƙarin zuwa Turai sun kasance cikin hadari a cikin kwale-kwalen roba 30 da wasu kwalekwalen katako 22.
An mika bakin hauren ba bisa ka'ida ba da aka ceto daga gabar tekun Morocco ga hukumomin da abin ya shafa domin aiwatar da ayyukan suka dace bayan taimakon farko.
A kowace shekara, dubban bakin haure ke tashi daga Afirka zuwa tekun Bahar Rum don isa Turai da fatan samun rayuwa mai kyau.