A ranar Alhamis ne majalisar Montenegro ta zartar da wani kuduri kan amincewa da kisan kare dangi a Srebrenica tare da yin watsi da ministan shari’ar kasar kan kalamansa na muhawara game da kisan kare dangin shekarar 1995 a Bosniya da Herzegovina.
Kudurin ya ayyana ranar 11 ga Yuli a matsayin ranar makoki da kuma tunawa da wadanda aka kashe a kisan kare dangi na 1995 na Musulmai maza da yara sama da 8,000, kuma majalisar za ta yi Allah wadai da duk wani musun kisan kare dangi a bainar jama'a.
Kudurin ya samu amincewa da kuri’u 55 na nuna goyon baya, 19 suka ki amincewa shida suka kaurace.
Majalisar har ila yau ta kada kuri’ar sallamar Ministan Shari’a da ‘Yancin Dan Adam Vladimir Leposavic saboda kalamansa na rashin fahimta da ya yi kwanan nan inda ya yi tambaya kan ko kisan kiyashin na Srebrenica ya faru.
Leposavic ya ce a shirye yake ya bayyana cewa an yi kisan kare dangi a Srebrenica "lokacin da aka tabbatar da shi ba tare da wata damuwa ba."
Wannan kalaman nasa ya janyo muhawara a kasar.