An kori manyan jami'ai a Saudiyya sanadiyar cin hanci da rashawa

An kori manyan jami'ai a Saudiyya sanadiyar cin hanci da rashawa

Ayayinda daraktan kula da iyakokin kasar Saudiyya ya ajiye mukaminsa bisa tuhumar cin hanci da rashawa an kuma kori jami’ai 5.

Kanfanin dillancin labaran SPA ta Saudiyya ta yada wata kasida da ta kunshi shirin yariman Saudiyya mai jiran gado Muhammed bin Selman na 'Tsarin 2030' da ya kunshi magance ayyukan da basu dace ba da kuma hana aikata cin hanci da rashawa a yankunan yawon shakatawa na red sea'

A dokar an sanya shugaban kula da iyakokin kasa Janar Awad bin Iyd bin Abde al-Belewi ayiye mukaminsa da kuma cire walin garuruwan Umluj da Al-Vajh daga mukaminsu.

Hukumar Bincike da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta kasar ta fara gudanar da bincike akan shugabanin da ake tuhuma da aikata cin hanci da rashawar.

 


News Source:   ()