A jihar Texas da ke Amurka an kori dan sanda Shaun Lucas daga aiki sakamakon samun sa da laifin kashe tsohon dan wasan kwallon kafa na kasar Jonathan Price.
Sanarwar da mahukuntan garin Wolfe City suka fitar ta ce an kori Lucas mai shekaru 22 daga aiki sakamakon laifin aikata kisan kai.
Sanarwar ta ce an kori Lucas saboda karya ka'İdar aikin 'yan sandan garin ta mummunan hanya.
Lauyan Price, Lee Merritt ya ce iyalan wanda aka kashe sun yi farin ciki sakamakon korar Lucas daga aiki, kuma tuntuni ya kamata a ce an dauki wannan mataki.
A daren wata Asabar ne bayan korafin cacar baki da ake yi da Price bakar fata, sai dan sanda Lucas ya je wajen tare da kokarin kama shi.
Price mai shekaru 31 da ya fito daga shagon da ya ke cikin hannayensa a sama, ya so ya nesanta kansa daga dan sandan. Amma nan da dan sanda Lucas ya dauki bindiga tare kashe shi.