An kori 'yar jaridar da ta nuna cewa ta shiga cikin ayyukan agaji ta hanyar shafa wa kanta laka a yayin da take aikin yada labarai a yankin da ambaliyar ta shafa a Jamus.
Ambaliyar da aka yi sakamakon ruwan sama mai karfi wanda ta shafi yammacin Turai ta haifar da asarar rayuka.
Yayinda Jamus, kasar da ambaliyar ta fi shafa, ke ƙoƙarin warkar da raunukan da bala'in ya haifar, labarin wani 'yar rahoto ya zama abin tattaunawa.
Bidiyon wata 'yar jaridar RTL Susanna Ohlen, wacce ta je yankin da bala'in ya faru, ya zama ajanda a ƙasar.
Ohlen ta yi tattaki zuwa yankin da ambaliyar ruwa ta lalata a jihar North Rhine-Westphalia. Tare da yin labarin cewa ta halarci aikin sadaukarwa a can.
Don kara amincin labarinta, ta rinka shafawa kanta laka. A wannan lokacin, ba ta san cewa wani yana kusa da ita ba.
A cikin dan kankanen lokaci dai wannan bidiyon ta na shawa kanta tabo ya yadu a shafukan sada zumunta.
A cikin wata sanarwa daga RTL,
"Wannan aikin da wakiliyarmu ta yi ya yi hannun riga da ka'idojin aikin jarida da kuma fahimtarmu game da aikin jarida."
An lura cewa an kori Ohlen mai shekaru 39, wacce ke aiki a RTL tun shekarar 2008.