An kori 'yan ta'addar PKK daga gundumar Sinjar

An kori 'yan ta'addar PKK daga gundumar Sinjar

An kori 'yan kungiyar ta'addar a ware ta PKK daga gundumar Sinjar da ke lardin Mosul a Iraki.

Sojojin tarayya da ke da alaka da gwamnatin tsakiya sun fara zama a cikin cibiyoyin jama'a.

Sojojin tarayya wadanda aka fara aikawa zuwa gundumar daga awannin safiya sun mamye duka ofisoshin hukuma da rana.

Ana sa ran gwamnatin tsakiyar Baghdad za ta fitar da sanarwa a hukumance bayan da aka tsarkake cibiyar gundumar da dukkan kungiyoyin da ke kewayenta. 

Ana ci gaba da shirye-shiryen dawowar mutanen yankin Sinjar.

An sanya hannu kan Yarjejeniyar Sinjar tsakanin Bagadaza da Erbil a watan Oktoba wacce ta tanadi kawar da kungiyar ta'adda ta PKK daga yankin. A karkashin yarjejeniyar, dole ne duk haramtattun abubuwa su bar yankin.


News Source:   ()