An kona wata cibiyar yin allurar riga-kafin Corona a Faransa

An kona wata cibiyar yin allurar riga-kafin Corona a Faransa

A garin Bayonne da ke Faransa an kona wata cibiyar yin allurar riga-kafin Corona.

Labaran da France Bleu Pays Basque suka fitar na cewa, a daren Lahadin nan ne aka ga cibiyar allurar riga-kafin Corona da ke Urrugne a garin Bayonne ta fara ci da wuta.

Jami'an kashe gobara sun kashe wutar kafin ya cinye cibiyar baki daya.

Binciken farko da aka gudanar ya nuna an barbada man fetur a cibiyar tare da cinna mata wuta.

Ofishin gabatar da kara ya fara gudanar da bincike bayan rahoton da ya karba daga wajen 'yan sandan Bayonne.

A ranar 2 ga Yuli a garin Nice na Faransa masu adawa da allurar riga-kafin Corona sun yi rubutun batanci a jikin tantunan yin allurar.

A makon da ya gabata Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron ya bayyana za a tilastawa dukkan ma'aikatan lafiya karbar allurar riga-kafin Corona, kuma za a fadada bayar da katinan shaidar yin allurar a kasar.

Bayan kalaman na Macron an gudanar da zanga-zangar adawa da allura da katin Corona a garuruwan Faransa da dama.


News Source:   ()