An kawo karshen hare hare da amon wuta a Gaza

An kawo karshen hare hare da amon wuta a Gaza

Mazauna yankin Gaza da kuma jami'an kul ada lafiya sun ce sun daina jin amon wuta ko karara fashe fashe sakamakon hare haren saman da Isra'ila ta dauki dogon lokaci tana kai wa yankin.

Wasu bayanai na daban kuma sun ce Isra'ilar ta kai wasu hare hare a arewacin Gaza, inda suka yi sanadiyar kashe mutane 13 da kuma raunata wasu da dama.

Da farko dai Isra'ilar ta zargi kungiyar Hamas da tsaikon da aka samu wajen aiwatar da yarjejeniyar da aka shirya fara aiki da ita da misalin karfe 6.30 na safiyar yau, saboda jinkirin da aka samu na gabatar da sunayen Yahudawa 3 da kungiyar za ta sake a matsayin kashi na farko na firsinonin dake hannun ta.

Wasu mazauna Paris ke zanga zanga dauke da hotunan mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su a Gaza Wasu mazauna Paris ke zanga zanga dauke da hotunan mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su a Gaza AP - Aurelien Morissard

Ministan harkokin wajen Isra'ila Gideon Saar ya ce tun a jiya ake saran Hamas ta gabatar da sunayen amma bata yi haka ba har sai bayan sa'oi 18, abinda ya sa aka samu tsaiko.

Wani jami'in Falasdinu ya zargi Isra'ila da tsaikon da aka samu na gabatar da sunayen saboda hare haren da jiragen ta suna ci gaba da kai wa a yankin.

Wata sanarwar da Hamas ta gabatar sa'oi 2 bayan lokacin aiwatar da yarjejeniyar ya kunshi sunayen Yahudawa guda 3 da kungiyar za ta sake da suka hada da Romi Gonen da Doron Steinbrecher da kuma Emily Damari.

Ana saran wannan yarjejeniyar da za'a kwashe kwanaki 42 an aaiwatar da ita ta bude kofar kawo karshen yakin Gaza baki daya.

Hukumomin Falasdinu sun ce mutane kusan dubu 47 Isra'ila ta kashe a wannan yakin da aka kwashe watanni 15 ana fafatawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)