An kashe 'yan ta'addar YPG/PKK guda uku a yayin samamen jiragen sama da na kasa a arewacin Iraki da Siriya.
Ma'aikatar ta sanar a kafafen sada zumunta cewa an kawar da biyu daga cikin 'yan ta'addan ta hanyar kai hare-hare ta sama a yankin Gara na arewacin Iraki yayin da ake ci gaba da ayyukan yaki da ta'addanci a kasar.
Sauran 'yan ta'addar, wadanda ke da alaka da YPG - reshen kungiyar ta'addar PKK dake Siriya an kashe a yayinda da suke yunkurin yin kutse a yankin da Turkiyya ta kaddamar da farmakin Tafkin Zaman Lafiya a shekarar 2019.