A yankin Farmakan Reshen Zaitin da ke arewacin Siriya an kassara 'yan ta'addar na YPG/PKK 2 a lokacin da suka shirya kai hari.
Shafin Twitter na Ma'aikatar Tsaron Kasa ta Turkiyya ya shaida cewa,
"Ba mu bar jinin Shahidanmu a kasa kawai ba, ba za kuma mu bari ba! Aiyuka kai farmakai da lalata matsgunan 'yan ta'adda na ci gaba a Yankin Farmakan reshen Zaitin. An kashe wasu 'yan ta'adda 2 da aka gano shirin kai hari a yankin."
Ma'aikatar Tsaron Turkiyya ta sanar da Shahadar sojojinta 2 a wani hari da 'yan ta'addar YPG/PKK suka kai a yankin Farmakan Reshen Zaitin na Siriya, kuma an mayar da martani inda aka kashe 'yan ta'adda 3.
Tare da hakan, an kashe jimillar 'yan ta'adda 5 a yankin.